Duk lokacin da aka yi zancen gwamnati, nan take tunaninmu ya kan koma ga irin gwamnatocin da ‘yan adam suke gudanarwa. Sai mu fara tunanin shugaban al’umma ko kasa, ko kuma sarkin gari, ko gwamnar jiha, da dai sauransu.
Wadannan duka sun taso ne daga tsare-tsare ko kuma shirye-shiryen siyasa da kadamar da mulkokin da ‘yan adam suka kirkiro; kowace kasa ko al’umma da irin tsarinsu ko shirinsu.
Amma da manufa daya ce ake kafa gwamnati da kuma gudanar da shi; watau yadda za a tafiyarda ko kuma kula da rayuwar jama’ar da ke kalkashin gwamnatin ko kuma mulkin.
Wannan ya shafi biyan bukatar al’umma ta fannonin zaman lafiya da salama, tanadarda kayayyakin masarufi da tabbatar da jin dadin jama'a ta rayuwar yau da kullum da dai sauransu.
Bisa ga nazarinmu, mun gane gwamnatocin ‘yan adam a duk fadin duniya suna faman aiwatar da wadannan tsare-tsarensu. Amma tambaya a nan ita ce, shin, gudanarwar tana wadatar da jama’a yadda aka sa rai?
Ko jama’a sun gamsu da yadda shugabanansu suke tafiyarda al’amuran kasashensu? A kashin gaskiya, babu gwamnatin ‘yan adam, duk fadin duniya da ya iya biyan bukatun takalawa yadda ya wajaba.
Akwai wadanda suke anfani da sunan Allah, ko morar addini wai don su iya mallaki al’umma. An sami mulkoki iri-iri, kamarsu dimokaradiya, da mulkin danniya ko kama karya, da mulkin gurguzu da sauransu.
Amma, kash! A kwana a tashi, har wa yau ba a kai labari ba. Yanzu haka babu kome duk fadin duniya, sai hargitsu, tawaye, tashin hankali da rashin zaman lafiya. Wannan ke tabbatar da rashin gamsuwar jama’a game da gwamnatocin duniya.
To, yanzu ga wa za mu koma? Ina muka nufa? Dalilin rubuta wannan ‘yar takarda kenan. Babu abin da ya rage, illa a koma ga Ubangiji Allah ta wurin shaidar Mai Ceto Yesu Almasihu.
Muna da mabiyan Almasihu da suke cikin siyasar duniya; har an jima ana kokartawa ko zai yiwu a mori tafarkin Ubangiji a cikin siyasar duniya. Amma da ya ke al’amarin ya kumshi tsare-tsaren duniya ne, babu yadda za a ‘zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofofin salkuna’ (Markus 2:22). Ko kuma, me ya hada haske da duhu? (2Kor.6:14).
Abin nazari shine, sai da aka gama kulle-kulle duka sa'annan aka gayyace mu tafiya tare. Da muka zo tafiyar, sai muka tarar muna famar gini bisa rairayi ne kawai.
Abin nufi shine, akan harhada
dukan kungiyoyi dabam dabam kafin a fito da tsarin siyasa da kuma kundin tsarin kasa. A ciki sai a nanata cewar ‘ba ruwan wannan tsarin da sha’anin addini.’
To, in kuwa haka ne, ina matsayin Kirista game da wannan al’amari? Shi ya sa in ana taron siyasa, sai ka ji riya da yaudara, ‘Kungiyoyin addinai da suke da wakilci a wannan taron za su yi mana addu’a;’ alhali kuwa ba a ma amince da juna ba.
Ko a jihohin da suke da mabiyan wani addini mafi yawa, ba su da ‘yanci ko rinjayi wajen karfafa bangaskiyarsu a taron siyasa.
Shi ya sa ya zama dole mu koma ga tsarin mulkin Allah cikin Yesu Kiristi ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Ta yaya haka zai yiwu? Za mu kafa wani gwamnatin da zai saba da tsarin yanzu? Me za mu yi da shiryen shiryen da ake aiki da su yanzu? Za mu daina zaman ‘yan kasar don mu iya gudanar da Mulkin Allah ke nan?
{Idan kana da ra’ayi ko shawara game da wannan shiri, sai ka rubuto mana ta adireshinmu.} (za mu cigaba…)