Mun dade muna rikicewa, muna kuma cikin duhu da jahilci. Ga kuma bayani a fili game da koyaswar YESU ALMASIHU Dan ALLAH Rayayye game da babbar Kalmar nan ta BANGASKIYA.
Muryar UBANGIJI na Magana da mu a cikin 1Korantiyawa 2:5-7, “Kada bangaskiya mu ta dogara ga hikima mutane, sai ga karfin ALLAH. Duk da haka dai muna sanar da hikima ga wandanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani nan, wadanda suke shudewa ba. Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta ALLAH wadda da boyayyiya ce, wato, hikimar da ALLAH ya kaddara tun gaban farko zamanai, domin daukakarmu”
In dai ayar na karfafamu haka, don me muke saurarar hikimar duniya? YESU ya ce mu gaskanta da ALLAH, ”Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskantawa da ni, ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har zai yi ayyukan da suka fi wadannan” (Yahaya 14:12). Sai mu zama masu aikata nufinsa.
IBRANIYAWA 11:1-3 “To bangaskiya kuwa ita ce hakkakewar abubuwan da ake bege a kai, ita ce kuma tabbatawar abubuwa da ba a gani ba.Ta wurin bandaskiya mun fahimta, cewa ta fadar ALLAH ce aka tsara duniya, har ma abubuwan da ake gani, daga abubuwan da ba a gani ne suka kasance” ‘Yan’uwa mun bata fa in ba tare da bangaskiya ga YESU ALMASIHU ba. Ta yaya za mu dogara ga wani ko kuwa hikimar wani, mu kira shi bangaskiya? Karatu ba biyaya, tawaye da kuma aikin banza ne. “Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce”(YAKUBU 2:17).
Kada a ce da mu, “Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gaba ce da ALLAH ba? Soboda haka, duk mai son abuta da duniya, ya mai da kansa mai gaba da ALLAH ke nan.” (YAKUBU 4:4).
YESU ya ba mu iko ta wurin bangaskiyan nan, mu fitar da bakaken aljannu, mu warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya, mu ta da mattatu, mu tsarkake kutare, mu kuma fitar da al,jannu, kyauta aka ba mu, mu kuma bayar kyauta. MATIYU 10:8. To shin, me mu ke yi? Haba jama’a mu koma kan gaskiya.
KIYAYEWA A SAUKAKKE
“Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunen duniya” (WAHAYIN YAHAYA 3:10). “Duk wanda ya je wurin Madaukaki zai zauna lafiya, hakika zai kiyaye ka daga dukan hatsororin da ke boye, daga kuma dukan mungayen cuce-cuce zai rufe ka da fikafikansa, za ka zauna lafiya a karkashinsa. Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka har abada” (ZABURA91:1-4).
Don haka, duk mai gaskantawa da YESU, kada ya yi zaman duhu. Ga kashedin Manzo Bulus, “Ya ku mutane marasa azanci wa ya dauke hankalin ku? Ku da aka bayyana maku YESU ALMASIHU gicciyeyye sosai, ashe rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku karasa? Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banza ne! wato, shi da yake yi mana baiwar Ruhu, yake kuma yin mu’ujizai a cikinku, saboda bin shari’a ne ya ke yin haka, ko kuwa saboda gaskantawa da Magana da kuka ji.” (GALATIWA 3:1-6)
“Haka ma Ibrahim ya gaskata ALLAH, bangaskiya nan tasa kuma, aka lisafta adalci ce a gare shi, aka kuma kira shi aminin ALLAH.” (YAKUBU 2:23). Idan mun yi biyayya, za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarnnisa, kowa ya ce ya san shi, baya kuwa bin umarnnisa, makaryaci ne, gaskiya kuma bata tare da shi. Bari mu yarda da ikon tashinsa daga matattu, kada mu zama masu shakka. Bari Ruhunsa ya bi da mu har abada abadin a cikin Sunan Yesu. AMIN, AMIN!