Wednesday 27 June 2018

MULKIN UBANGIJI






Duk lokacin da aka yi zancen gwamnati, nan take tunaninmu ya kan koma ga irin gwamnatocin da ‘yan adam suke gudanarwa. Sai mu fara tunanin shugaban al’umma ko kasa, ko kuma sarkin gari, ko gwamnar jiha, da dai sauransu.

Wadannan duka sun taso ne daga tsare-tsare ko kuma shirye-shiryen siyasa da kadamar da mulkokin da ‘yan adam suka kirkiro; kowace kasa ko al’umma da irin tsarinsu ko shirinsu.

 Amma da manufa daya ce ake kafa gwamnati da kuma gudanar da shi; watau yadda za  a tafiyarda ko kuma kula da rayuwar jama’ar da ke kalkashin gwamnatin ko kuma mulkin.

 Wannan ya shafi biyan bukatar al’umma ta fannonin zaman lafiya da salama, tanadarda kayayyakin masarufi da tabbatar da jin dadin jama'a ta rayuwar yau da kullum da dai sauransu.

Bisa ga nazarinmu, mun gane gwamnatocin ‘yan adam a duk fadin duniya suna faman aiwatar da wadannan tsare-tsarensu. Amma tambaya a nan ita  ce, shin, gudanarwar tana wadatar da jama’a yadda aka sa rai?

 Ko jama’a sun gamsu da yadda shugabanansu suke tafiyarda al’amuran kasashensu? A kashin gaskiya, babu gwamnatin ‘yan adam, duk fadin duniya da  ya iya biyan bukatun takalawa yadda ya wajaba.

 Akwai wadanda suke anfani da sunan Allah, ko morar addini wai don su iya mallaki al’umma. An sami mulkoki iri-iri, kamarsu dimokaradiya, da mulkin danniya ko kama karya, da mulkin gurguzu da sauransu.

 Amma, kash! A kwana a tashi, har wa yau  ba  a kai labari ba. Yanzu haka babu kome duk fadin duniya, sai hargitsu, tawaye, tashin hankali da rashin zaman lafiya. Wannan ke tabbatar da rashin gamsuwar jama’a game da gwamnatocin duniya.

To, yanzu ga wa za mu koma? Ina muka nufa? Dalilin rubuta wannan ‘yar takarda kenan. Babu abin da ya rage, illa a koma ga Ubangiji Allah ta wurin shaidar Mai Ceto Yesu Almasihu.

Muna da mabiyan Almasihu da suke cikin siyasar duniya; har an jima ana kokartawa ko zai yiwu a mori tafarkin Ubangiji a cikin siyasar duniya. Amma da  ya ke al’amarin ya kumshi tsare-tsaren duniya ne, babu yadda za a ‘zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofofin salkuna’ (Markus 2:22). Ko kuma, me ya hada haske da duhu? (2Kor.6:14). 

 Abin nazari shine, sai da aka gama kulle-kulle duka sa'annan aka gayyace mu tafiya tare. Da muka zo tafiyar, sai muka tarar muna famar gini bisa rairayi ne kawai.

Abin nufi shine, akan harhada
dukan kungiyoyi dabam dabam kafin a fito da tsarin siyasa da kuma kundin tsarin kasa. A ciki sai a nanata cewar ‘ba ruwan wannan tsarin  da sha’anin addini.’

 To, in kuwa haka ne, ina matsayin Kirista game da wannan al’amari? Shi ya sa in ana taron siyasa, sai ka ji riya da yaudara, ‘Kungiyoyin addinai da suke da wakilci a wannan taron za su yi mana addu’a;’ alhali kuwa ba a ma  amince da juna ba.

 Ko a jihohin da suke da mabiyan wani addini mafi yawa, ba  su da ‘yanci ko rinjayi wajen karfafa bangaskiyarsu a taron siyasa.
 Shi ya  sa ya zama dole mu koma ga tsarin mulkin Allah cikin Yesu Kiristi ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

 Ta yaya haka zai yiwu?  Za mu kafa wani gwamnatin da zai saba da tsarin yanzu? Me za mu yi da shiryen shiryen da ake aiki da su yanzu? Za mu daina zaman ‘yan kasar don mu iya gudanar da Mulkin Allah ke nan?

{Idan kana da ra’ayi ko shawara game da wannan shiri, sai ka rubuto mana ta adireshinmu.}  (za mu cigaba…)


Monday 25 June 2018

BAIWAR HARSUNA


 

The Spirit’s Voice       www.boilingpointgospelcentre.org February 10, 2015 Translated by Bro Matthew Arin Adams   

Yadda Shaidan ya ke hana Kirista karbar Baiwar Addu’a  Cikin Harsuna
Addu’a cikin Harsuna.

Shaidan ya yi nasara cikin yayata karyar hana Kirista samun Baiwar Harsuna. Akwai karairayi da yawan gaske da rashin fahimta a cikin ikilisiya game da wannan baiwar.

A takaice, bai dami Shaidan ba, idan Ikilisiya tana magana a kan baiwar, a yi nazari a kai, da yin mahawara a kai, a kuma yi tattaunawar rukunai a kai, amma ba zai taba yarda su karbi baiwar ba.

Ina amfanin sojar da ya ke da ilimi ko sani game da bindigogi, amma shi kansa ba shi da ko guda daya?

Rashin amfani da wannan Baiwar ta gurgunta Ikilisiya, wannan ne dalilin rashin ci gaba da girman masu ba da gaskiya da yawa ta kaiwa ga Ingantattun Baye-baye. Lokaci ya yi da zamu mori Baye-bayen da Ubangiji ya ba mu.

Idan kai Kirista wadda ba shi da baiwar Addu’a cikin Harsuna… Ya kamata ka samu. Kada ka ci gaba da ba da hujjojin cewar ba ka bukatarta, ko kuma yadda ka nema amma kuma ba ka samu ba. KAI DAI KA KARBI BAIWAR!

Idan ka rigaya ka karbi baiwar… Yi Amfani da ita. Ka Rura ko Zuga ta. Babu riba a ciki idan ta kwanta ko barci. Bari mu dubi wadansu KARAIRAYIN da suka hana Kirista karbar wannan baiwar.

Karya Lamba ta 1
"Wannan daga Ibilis ne, shi ne ya ke Magana ta gareka."

Babu wani misali a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewar baiwar harsuna na zuwa daga wurin Shaidan ne. Karanta 1Korintiyawa 12:3; Karanta 1Korintiyawa 14:14

Karya Lamba ta 2

"Wai baiwar ba ta kowa da kowa ba ce."

Dalilin da ya karyata wannan tunanin shi ne kowane mutum a cikin ililisiyar farko ya karbi baiwar harsuna.
Bari mu dubi abin da Ayyukan Manzanni 2:1,4 ya ce, Karanta wadannan ayoyin.

Wani Pasto abokin aikina yana hidima a taron falkaswa inda mutane wadanda yawansu ta kai 300 suka fito gaba mussamman don karbar wannan baiwar. Bayan ya yi addu’a, duka 300 din suka karbi baiwar.

 To, macece hujjar cewar wannan baiwar ba na kowa da kowa ba sai dai na wadansu kima kawai? Baiwar na nan don dukan wadda ke da bangaskiyar karba.

Karya Lamba ta 3:

"Na rigaya na yi kokari, bai yiwu ba, ba zan iya karba ba."

Yadda na sami fahimta game da al’amarin, addu’ar minti biyar bai isa don samun baiwar ba. Mai yiwuwa ne wadansu pastoci da suke da shafewa mai karfi suna iya addu’a har a sami baiwar da sauri, amma yadda na sani, dole ne mai nema ya dauki lokaci cikin addu’a da naciya kafin ya samu.

Koyaswa game da wannan baiwa zai zuga bangaskiyar mutane har su karba. Ya kan zama wajibi ka yi addu’a fiye da sa’a daya kafin ka karba. Don haka akwai bukatar hakuri cikin jira.









Saturday 16 June 2018

EMPHASIS ON DEATH THAN LIFE


I came across this article on our website (June 2013 edition of the Spirit's Voice) and decided to post it on my blog; with no doubt in my heart that it will surely bless you!
This is not far from the incident that took place in the Temple at Jerusalem during the earthly ministry of Jesus; how He literally forced out ungodly practice from God’s House (Mt 21:12; Jn 2:15).
 For the Church to remain accessible and acceptable to God, it is supposed to follow every detailed biblical instruction. Believers are never what we are when we do things that are not according to injunctions spelt out in God’s Word; the Bible. Below are some of the things God’s people had fallen short of compliance;
  1. Emphasis on DEATH than LIFE: Our Master Jesus came that we may have life both abundant and eternal, contrary to Satan’s suggestions, the architect of all theft, sorrows, pain and death. (Jn 10:10). Our Lord, the very One we all claim to follow, did not bury the dead, but raised them that were dead. And He instructed His disciples, including the present day church; “Heal the sick, cleanse the lepers, raise the dead, cast out demons. Freely you have received, freely give.(Mt 10:8) Take a close look at the examples of the dead raised in the Bible:
Women had their dead raised – Heb 11:35; The son of the widow of Zarephath 1Ki 17:17-23; The Shunammite woman’s son 2Ki 4:32-37; The young man laid in Elisha’s grave 2Ki 13:21; The widow’s son Luke 7:12-15; Jairus’ daughter Luke 8:49-55; Lazarus John 11:43-44; Dorcas Acts 9:37-40; Eutychus Acts 20:9-12. -Nave’s Topics
There is still in Scripture an account of someone who was called by Jesus to follow Him, but sought an excuse to go and bury his father. “Then He said to another, “Follow Me.” But he said, “Lord, let me first go and bury my father.” Jesus said to him, “Let the dead bury their own dead, but you go and preach the kingdom of God.” (Lk 9:59-50). 
In other words, Jesus meant that those who are engaged in His affairs should not be involved in burying the dead; but should insist to follow Him and learn the secret or mysteries of the kingdom of God; operating in His nature; performing signs and wonders; or functioning in the scope of faith and Holy Spirit’s power (1Cor 12:7-10). 
This must sound as an affront and bizarre to the erring ministers whose ordination is only meant to officiate in burials, marriages and other ceremonial rites; which never formed part of the life and ministry of our Lord Jesus. 
The question that follows is, “Whose ministry are you imitating?” Why should Christians pay so much homage to funerals; making long vehicle convoys to burial scenes, instate of getting more serious about evangelism? 
When shall we see large gatherings; many people trooping for soul winning; saving lives than the ungodly preoccupation with death?! 
Another aspect of death celebration is the advertisement of caskets by the road sides. If the ungodly society approved of this evil, should the church permit or agree with members engaged in this terrible enterprise? Let us preach salvation, let’s save lives.