Monday, 16 December 2019

MATSAYIN KOWANE KRISTA


Abin takaici ne ganin Kirista da yawa suna rayuwa cikin kunya da tsoro saboda rashin sani; rashin fahimtar matsayinsu na ainihin nufin Ubangiji don rayuwansu da hidimarsu cikin ikkilisiya. Manufar kowane mai bi ita ce ainihin kwaikwayon ko bin gurbin rayuwar Almasihu tsan-tsan. Duk wani abu waje da wannan, addini ne kawai ba bi na gaskiya ba ne.

Yawancin Kirista har yanzu suna tunanin cewa Almasihu ya zo don gabatar da wani addini ne, kuma wannan shine dalilin da ya sa ake daukar kowane aiki a cikin ikilisiya a matsayin hidima ko ibada ga Ubangiji. Wannan ba daidai ba ne, babban kuskure ne game da rayuwar bin Yesu Kiristi da aikinsa.

Idan masu bi sun zama kamar Yesu a duk abin da suke yi, to ya zama tilas a fahimci hidimar sa. "Za ta haifi ɗa, za ka sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” (Mt 1:21).
Ma'anar Sunan Yesu cikin Ibrananci ita ce Mai Ceto. Sabili da haka, aikin hidimar Ubangijinmu Yesu shine ya kubutar damu daga zunubanmu.

Ba shakka, a matsayin masu bi, dole ne mu riga sanin wajibcin ceton mu.Da zaran mun sami ceto, nan take aka kiramu zuwa ceton wasu ke nan.
“...In kun ci gaba cikin maganata, hakika ku ne almajiraina…" (Yahaya 8:30).
Ya kamata kowane mai bi ya dage da bangaskiya ga Allah ta wurin Kiristi Yesu. Ci gaban bangaskiyar mu ta bishewar Ruhu Mai Tsarki yana tabbatar da babban aiki a cikin biyayya da koyarwar Jagora, watau Almasihu ke nan, sai kuma nacewa ga karbar aikin zaman almajiransa ba tare da wata shakka ko jayayya ba.

Dole ne mu magance matsalar da ta sa Krista da yawa su ke sake komawa cikin ragonci, sakkaci da lalacewa. Wannan tunanin cewar ainihin hidimar Yesu; wa’azi, koyarwa, warkar da marasa lafiya, da sauransu na pastoci ne kawai ba daidai ba ne ko kayan.
Wannan ba hanyar da Ubangiji yayi niyyar aiwatarwa ba.

“Yanzu ku jikin Almasihu ne, gaɓoɓi kuma musamman.” (1Kor 12:27).

A matsayin mu na jikin Kristi, babu wani a cikinmu da ba shi cikin wannan gatan kulawa mai ban mamaki ba. Ubangiji yana taimako da bishewa ga dukan Kirista!

"A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri." (1 Kor 12.28)

Mecece manufar wannan? “Hakanan ku, duk da cewa kuna ɗokin kyautar bayebaye na ruhaniya, ku nema don ku fifita wajen inganta ikkilisiya.” (1Kor 14:12). Inganta Ikilisiya ita ce cigaban Mulkin Allah ne da adalcinsa a nan duniya. Kuma wannan aikin yana rataye a wuyan kowane mai bi!

Ga misalin da Yesu ya bai wa almajirai na farko da ya aike su wa'azi a cikin Matiyu 10. “Kuma kuna zuwa, wa'azin, kuna cewa, Mulkin Sama ya kusato. Ku warkar da marasa lafiya, ku tsarkake kutare, ku ta da matattu, ku fitar da aljannu: an ba ku kyauta, ku bayar kyauta." (Ayoyi 7,8).

Waɗannan almajirai ba pastoci ko annabawa ba ne a lokacin. Amma mabiyan Yesu ne kawai. Sun dai yi biyayya ga gayyatarsa da bin koyarwarsa, wannan ya sa suka kware ga ayyukan al'ajibai. Wannan shi ne abin da ake sa rai game da dukan Kirista.

Idan Ikklisiya zata rungumi tsarin Ubangiji game da hidima, da yawa cikin Krista baza su zama masu zaman kashe wando ba; suna wasan dara da ludo, da sauran wasannin yau da kullun ba; zasu kuma dena zaman masu bin ranar Lahadi kawai. Amma za su kasance masu Bishara kowace rana!

Menene matsayin shugabanin Ikklisiya? Wannan har yanzu yana da kyau; yana da matukar muhimmanci. Makiyaya yakamata su kwaikwayi Jagoransu Yesu Almasihu, watau su aikata irin ayyukansa da ya yi duka har ma fiye da haka. (Yahaya 14:12).

Ubangiji ya koya mana mu jagoranci garken a matsayin ma'aikata na gari da tabbatar da cewa babu wani sashin jikin da yake lalacewa ko mara anfani, kuma kada a bai wa miyagun ruhohi dama su ci zarafin garken.

A karshe, dole ne masu bi su kai ga samun ingantaccen tabbacin cetonsu, su kuma kiyaye matsayin shaidar Kirista na bautar Ubangiji don ceton rayuka da kuma almajirtar da wasu.

Duk inda masu bi suka sami kansu, yakamata gurbin Yesu ya kasance dalilin ci gaba har a yi nasarar tsere haɗarin wutar jahannama.

Kuma mun sani cewa wannan shine ainihin dalilin zuwan
Kristi a duniya; domin kada mu lalace amma mu sami rai na har abada. (Yahaya 3:15-21).

No comments:

Post a Comment