Wednesday, 13 December 2023

AYOYI GAME DA WARKARWA


Mutane masu yawan gaske suna shakkar ikon Ubangiji na warkarwa. A gaskiya, dole ne mu dawo kan bangaskiyar da zai faranta wa Ubangiji rai. (Ibraniyawa 11:6)  

Karanta wadannan ayoyi don samun karfafawa da karfin halin yin bangaskiyar dogara ga ikon Ubangiji na warkarwa.

Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa. (Far 20.17)

Ishaku kuwa ya yi addu'a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki. (Far 25.21)

Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.” Fit 15.26

Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo. A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai. (Fit 23.25-26)

“ ‘Ku duba fa, ni ne shi, Ba wani Allah, banda ni, Nakan kashe, in rayar, Nakan sa rauni, nakan kuma warkar, Ba wanda zai cece su daga hannuna.” M. Sh 32.39

Sa'an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.” Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo. 1 Sar 17.21-22 

Sai ya tafi maɓuɓɓugar ruwa yana barbaɗa gishirin, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da wannan ruwa, ba zai ƙara sa a mutu ko a yi ɓari ba.’ ” 2 Sar 2.21

A cikin Littafin 2 Sar 4: 32-36, Annabi Ilisha ya rayar da Dan Bashumeriyar daga mutuwa. 

“Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Uba

ngiji.” 2 Sar 20.5

No comments:

Post a Comment