Monday, 15 June 2020

MULKIN ALLAH A DUNIYA



Dauki mintoci kaɗan ka karanta addu'ar da Kiristi Yesu ya gabatarwa masu binsa; watau, Addu'ar Ubangiji.

“...Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki. Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.” (Mt 6: 9, 10)

Menene fahimtarka, fassararka da amincewarka game da “... A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama ...”? Amsarka zai tabbatar da yadda kake morar wannan Addu'ar a cikin rayuwarka ta yau da kullun

Mun nace kan wannan batun domin wahayi ne da ya dade kuma ya kasance a birnin zuciyar shirin Ubangiji ta wurin Kiristi don ya ba Ikilisiyarsa da al'ummar duniya matsayin karshe cike da nasara da ikon cikin hali na karshen da ake ciki. Wutar farkaswar na kan ci, babu mai iya tsayarda ita, kuma mutane da yawa sun kamu da harsunan wutar da za ta mayar da tsarin Mulkin Allah a gurbin ta a cikin duniya!

Fidda zuciya, rudani da rashin bege a bayyane suke a fuskokin mutane da yawa a duk fadin duniya a yau! Sai kuma tsananin Kaunar Duniya ta rinjayi mutane masu yawan gaske, dogara ga Ubangiji ya rasa fifiko a tsakanin mabiyan Almasihu. Wannan shine ya jawo la'ana da ba'a da kunya ga Ikilisiyarsa.

Kowane mai gaskiya a Ruhaniya zai iya gane da abin da ke gudana game da wannan halin koma baya da lalacewar; sai ga Magadan Ubangiji da ake tsammanin za su wakilce shi ta bayyana ikonsa, sai aka mai da su abin zargi a fuskar duniya!

Me ya sa haka? Gaskiyar ita ce, idan tsarin duniya ya fi mallakar mutanen Allah, kuma muddin an yi watsi da ƙa’idodinsa da tsayayya da Maganarsa da ke kunshe cikin hidimar Kiristi, to, bin Yesu sai ya zama kamar addinin na al'ada, ba hanyar Gaskiya na ceton rayuka ba kuma. Wannan ya haifar da abin da ke faruwa a fagen siyasar duniya a yau wanda ya mamaye al'amuran Ikilisiyar Almasihu!

MULKIN DUNIYA GABA DA MULKIN ALMASIHU

Wannan batun yana buƙatar cikakken bayani da bincike. Amma a halin yanzu, gwargwadon wahayi na Ruhaniya da tabbataccen kwarewarsa, Gaskiya ba ta da wuyar samu da kuma bayyani!

Ta yaya Ikklisiya ta shiga siyasar duniya? Domin hidimar Kiristi da ka'idodinsa na Mulki a bayyane dalla-dalla suke. Ta yaya za a sami makarantun Kirista, sai a tartar don koyar da ilimin duniya da wayewa zamani ciki? Me ya faru da horarwar da ginuwa ta Ruhaniya, gwargwadon ainihin hanyar da Ubangiji Maɗaukaki ya yi tsari ta wurin Almasihu Yesu?

Me yasa duniyar marasa imani zata ƙirƙiro tsarin siyasa sa'annan ta gayyaci Ikilisiyar Almasihu ta sa hannu da kuma aikata ko gudanar da ita? (Wani lokacin ina mamakin ko ma akwai Kirista a wannan yanayin da farko!). Idan da farko mishaneri da majami'u 'yan asalin sun nace a kan bayyanar Mulkin Almasihu wanda aka bayyana a sarari cikin koyarwarsa a cikin Matiyu sura 5,6, & 7, da sauran nassoshi na Littafi Mai Tsarki da suka nanata batun gudanar da Mulkin Sama a Duniya, shin za a sake samun buƙatar zaɓin madadin wani abu da ake kira siyasa kuma?

Addu'ar Ubangiji ta kasance tare da mu tun daga lokacin da Almasihu Yesu ya ba da shi ga almajirai waɗanda su kuma suka mika ta zuwa ga Ikilisiyarsa. Tun daga wannan lokacin sai Addu'ar ta kasance haddacewa ne kawai, ko waƙa ko kalmomin ƙarshen taron sujada kawai! Ko da yake wannan batun ya kasance da tsawon shekaru da yawa, amma, don Daukakar Ubangiji, lokaci yayi da za a dawo kan aikin gaskiya da kuma amfani da shi!

Babban hakkin Mulkin Sama a Duniya shine tasirin da Addu'ar Ubangiji ya mika wa Ikklisiya da ya kamata ta yi a rayuwar wadanda suka yi himmar nacewa a kai da kuma aikata shi.

Bari wannan Addu'ar Samaniya ta mamaye duniya. Domin muna shelar Addu'ar Ubangiji tare da bangaskiyar samun fa'idodin sa na gaskiya a rayuwarmu da mulkin sa a kan duniya, wannan shine abin da Almasihu yayi nufin bada shi garemu.

"Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama"
(Mt 6:10).
Sama a duniya; kamar yadda muka furta Kiristi a duniya haka kuma a sama za a furta mu. Yadda kuma aka yi musunsa a nan duniya haka kuma za a yi musun mutum a Sama. (Luka 12: 8, 9)

Sama a duniya; Akwai wannan tabbacin cewa sama za ta aikata duk abin da muka yanke shawarar yi muddin akwai yarda game da abin muka kulla a nan duniya. Bangaskiyar shaidu biyu ko uku na iya tabbatar da amsawar Ubangiji ga addu'a da aikinsa a zahiri. (Mt 18: 18-20.)

Sama a duniya; "Hakanan ina gaya maku, akwai farin ciki a gaban mala'ikun Allah kan wani mai zunubi da ya tuba." (Lk 15:10.)

Sama a duniya; Tabbacin shiga Kursiyi ko Mazaunin Ubangiji Madaukaki cikin Almasihu cikin murna da Madawwamin farin ciki...
(Ibraniyawa 12: 22-24).

Sama a duniya;
“...Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan....suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa,"
(W. Yah 7.14-15)

Sama a duniya:
"...Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?"
(Ishaya 66: 1).

Tsarin Ikilisiya na duniya ba ya nufin komi ga Ubangiji; ginin gidan mu na ruhu ko zuciyar mu ya fi muhimmanci gareshi!

Sama a duniya; mu adana dukiyarmu a Sama; Zukatanmu kuma su kuɓuta daga jarabobin kayan duniya da munanan ayyukanta. (Mt 6: 20,21; 19:21.)

Sama a duniya; “...“Halleluya! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,
(W. Yah 19.1)

Gama Mulki da Iko da Girma na Ubangiji ne, daga yanzu har matukar zamani! Amin kuma Amin!

No comments:

Post a Comment