Thursday, 25 June 2020

MARTABAR HIDIMAR MASU BIN ALMASIHU (3)




Mutanen da ba sa son su dogara ga Ubangiji suna tunanin za su iya yin komai a cikin ikon kansu da kuma iliminsu. Wannan ko dai tawaye ne, girman kai ko kuma jahilci!

Bari mu yi zurfin nazari a kan koyarwa da hidimar Almasihu Yesu wanda har yanzu yake da matukar nacewa a kan bangaskiya!

Bari mu dubi wadansu ayoyi don karfafa  abubuwan da muka ambata a sama.
Ubangijinmu Yesu yana wa masu sauraronsa kashedi a kan marasa bada gaskiya har da mu na zamanin yanzu;
 "To, ga shi, Ubangiji yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!" (Mat 6.30)

 Dole ne mu koyi dogara ga Ubangiji game da dukan  al'amuran rayuwa. Kamar dai yadda ya ke magance bukatun dukkan halittarsa wadanda basu yin gwagwarmaya, haka ya fi kulawa da dukkan masu bangaskiya gareshi.

A wani sharhi na bangaskiya, Kiristi Yesu ya ji dadin bangaskiyar wannan jarumin;
 "Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, 'Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.'"
(Matta 8:10)
Bangaran ban sha'awar bangaskiyar jarumin yana cikin kalmominsa ga Yesu a cikin aya ta takwas; ".. .amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke." Ya gaskanta da ikon Maganar Kiristi da ya isa ya kai gun bawansa mara lafiya har ya warkar da shi.

Wannan shi ne irin bangaskiyar da ake bukata  daga kowane mai bin Yesu Almasihu!
Almajiran Yesu sun kasa fitar da aljannu daga wani yaron da aka kawo masu;
 "Sai Yesu ya amsa ya ce, 'Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.'"(Luka 9:41).

Daga baya, almajiran suka tambayi Yesu ko me yasa ba su iya fitar da aljanun ba.
"Sai ya ce musu, 'Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi'” (Markus 9:29)

Yawancin masu bi sun kasa aiwatar da hidimar Kiristi saboda rashin bangaskiya. Addu'a da Azumi na iya motsa karfin bangaskiya da ikon Ruhu Mai Tsarki don hidimar mu'ujizai. Ubangiji ya ceci  kowane mutum, ya kuma kira shi ya kuma kebe shi domin aiki cikin bangaskiya ta ikon Ruhu a cikin sunan Yesu. Tamkar, wannan shine matsayin kowane Kirista.

Bari mu yi addu'ar farkaswar bangaskiya da na zubowar  Ruhu Mai Tsarki don martabar hidimar Kiristi ya sauko kan Ikilisiya don cikakken aiki a cikin jama'ar Ubangiji. Amin

No comments:

Post a Comment