Saturday, 2 December 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 7)
1 SARAKUNA
18:12 Rabuwata da kai (Ilisha) ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni (Obadiya) baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji."

Obadiya ya rigaya ya san yadda Ruhun Ubangiji yake aikinsa a cikin annabi. Kamar yadda iska ke busowa, baka san inda ya fito da inda zata. (Yah 3:8). Bai kamata kowane mutum ya fahimci rayuwar wanda ke cikin Ruhu ba, sai wanda shima yana cikin Ruhu!

2:16  “…Bari mu tafi mu nemo maigidanka (Iliya), mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.” Elisha ya ce, 'Kada ku tafi.'"

Ko gaganci, ko rashin sani ne, ta yaya Ruhun Ubangiji zai jefar da annabinsa a kan dutse ko cikin kwari? Wadanda basu fahimci yadda Ruhu Mai Tsarki yake aiki ba sukan fadi abin da suka ga dama. Ubangiji kuwa baya jin dadin haka ko kadan. Shi yasa Yesu Almasihu ya yi kashedi game da zunubi gaba da Ruhun da babu gafartawa. 

No comments:

Post a Comment