61:1 “Ubangiji ya saukar mini da Ruhunsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.”
Tsarin koyaswa da rayuwar Almasihu a bayyane. Wannan ne ginshikin gudanar da Mulkinsa a duniya. Cikarsa ta tabbata da zuwansa a duniya; ya furta da kansa a cikin Luka 4:18. Da a ce masu binsa sun dauki wannan tsarin da muhimmanci, da duniyar siyasa da ilimi da kimiya da fasaha sun zuba mana ido suna mamaki da al’ajibi da girmama Ubangiji!
63:10 “amma suka yi masa tayarwa, suka cika Ruhunsa da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.”
Bata wa Ruhu Mai Tsarki rai daidai ne da sabon Ubangiji kansa. Duniya tana fuskantar barazana da masifu dayawa a yau domin an yi banza da shi da Ruhunsa. Za a iya samun sassautawa idan an gaggauta dawowa gareshi a cikin Sunan Yesu Almasihu. Amin!
No comments:
Post a Comment