Wednesday, 20 December 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 24)
FILIBIYAWA
1:19 “Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu”

Lafiya da taimakon Ruhu Yesu Almasihu? Aikin likita fa? Masu sayar da magani a kasuwa fa? Na sani duk inda ba a yardarwa Ruhu Mai Tsarki ba, ana iya neman taimako ko da ma gun Ibilis ne. Ubangiji ya mana jinkai a cikin Sunan Yesu Mai Cetonmu. Amin!

2:1 ”In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku,”

Tarayya ga Ruhu Mai Tsarki, dangantaka ce na kurkusa da naciya. Ina ake samun sahihiyar kauna, karfin hali, da karfafawa in ta Ruhun ba?

No comments:

Post a Comment