15:26 “Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni.”
Babu mashaidin Ubangiji na gaskiya sai dai wanda Ruhu Mai Tsarki ya mallake shi.
16:7-8 “Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.”
Zuwan Ruhu Mai Tsarki ya fi kasancewar Almasihu kansa a duniya. Shi zai kasance da gudanarda ayyukansa ko ina a lokaci daya a duk fadin duniyan nan. An rigaya an aiko shi, yana tare da mu. Yana kan aikin fadakarwa, falkaswa, warkaswa, da sauran al’ajibai. Kada rashin bangaskiya ya hana mu cin moriyar albarkunsa a cikin Sunan Yesu Almasihu. Amin!
16:13-14 “Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku. Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”
Aikin Ruhu Mai Tsarki shine bishewa ko kuma jagoranci zuwa cikin dukan gaskiya. Duk wani dan Adam da ke cewar shi mai fadin gaskiya ne amma ban da bishewar Ruhu Mai Tsarki, to, makaryaci ne. Bishewar Ruhun Ubangiji a cikin dukan ayyukanmu na daukaka Sunansa.
No comments:
Post a Comment