Wednesday, 29 November 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (29)



BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 6)
SAMA’ILA
1Samaila 10:6 “Sa'an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka (Saul), za ka yi annabci tare da su, a kuma mai  da kai  wani mutum dabam.”

10:9-10  “Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama'ila, sai Ubangiji ya ba shi (Saul) sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar. Sa'ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga annabci a tsakaninsu.”

Ta wurin bishewa Ruhun Ubangiji ne mai bin Yesu yakan  aikata al’ajibai. A nan sarki Saul, ba annabi bane, amma Ubangiji ya  sa yayi annabci. Ko kai ma zaka yarda Ubangiji ya more ka, idan ka gaskanta, don cikakken nufinsa ne ya more ka da wannan ikon Ruhu.

11:6  “Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.”
Duk lokacin da Ruhun Ubangiji ya sauko akan mai bin Yesu, ko ya husata, ba shi aikata mugunta, sai dai Ubangiji ya more shi ta hanyar nasara da daukakar Sunansa. 

18:13  “Sama'ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban 'yan'uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama'ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.”

Shafewar Dauda a matsayin Sarki ya zo ta bishewar Ruhu Mai Tsarki. Da Ruhun Ubangiiji, matsayin kowane mai bin Yesu na sarauta ne da zaman firist don hidimarsa cikin iko ba a cikin mutuntaka ba.

No comments:

Post a Comment