Sunday, 26 November 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 3)
LITTAFIN KIDAYA

 11:17 "Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin Ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai."
Ruhun Ubangiji ne a cikin Musa. Da shi za a rarraba wa ma’aikata don gudanar da aiki, don Musa ya sami saukin aikin. Idan Ruhu Mai Tsarki na aiki a cikin masu bin Yesu a cikin Ikilisiya, shugabanai ba za su sami yawan damuwa game tafiyar da ayyuka ba.

11:25 "Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa Ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da Ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba."
Aikin Ruhu Mai Tsarki shine ya iza ma’aikata ga aikata mu’ujizai ta morar baye-bayensa. A nan, dattawan sun cika da Ruhu, har suka yi annabci. Me zai hana wannan faruwa a cikin Iklisiyoyinmu yau? Har fiye da haka, na gaskanta yana iya faruwa!

11:26  "...Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon."
Muddin akwai izawar Ruhu Mai Tsarki, to, ko ina mutum yake zai iya morar baye-bayensa don inganta jama’ar Ubangiji.

No comments:

Post a Comment