BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 5)
LITTAFIN MAHUKUNTA
3:10 "Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa (Otniyel) domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi."
Don kyakyawan hukunci da nasara cikin yaki, Otniyel ya dogara ga bishewar Ruhu Mai Tsarki. Rashin adalci a duniya har ma cikin Ikilisiya ya rataya ne akan rashin sani da bishewar Ruhun Ubangiji.
6:34 "Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi."
Bishewar Ruhu Mai Tsarki ya sa Gidiyon ya aikata al’jibi; ya sami goyon bayan mutanen Abiyezer. Wani lokaci mutane sukan gwammaci dogara ga mutane a yanayin damuwa fiye da dogara ga Ubangiji, sai a karasa da karin damuwa da bakin ciki!
11:29 "Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa."
Bai zama wajibi Yefta ya sake rantse wa Ubangiji (aya 30) bayan ya sami bishewar Ruhunsa ba; wannan ya jawo masa mutuwar ‘yarsa. Bai kamata a yi wani aikin rashin bangaskiya sa’anda an sami tabbacin Ruhu Mai Tsarki ba!
No comments:
Post a Comment