Thursday, 23 November 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



Daga Matthew Arin Adams
Sanin Ruhu Mai Tsarki da ayyukansa a cikin Kirista...

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 1)
FARAWA
1:2 "Duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Ubangiji kuma yana shawagi bisa ruwayen”
Farkon halitta ke nan, Ubangiji kansa ya bukaci Ruhunsa ya yi nasa aiki kafin shi ya yi furcinsa game da halittar duniya.

6:3 "Sai Ubangiji ya ce, 'Ruhuna ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.' ”
Ta wurin Ruhu Mai Tsarki ne Ubangiji ya yi wa dan adam jinkai. Mu yi addu’a cewar, komen kasawa da rashin karfi, bari Ruhun Ubangiji ya iza mu cikin dukan al’amuranmu a cikin Sunan Yesu. Amin!

 41:38 "Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, 'Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Ubangiji yake cikinsa?'" Kwarewar Yusufu da hikimarsa daga Ruhu Mai Tsarki ne. Fir’auna ma ya gane da haka. Muna bukatar  bishewar  Ruhun Ubangiji don iya tafiyarda ayyukanda aka bamu. Sarakunan duniya suna iya ganin ikon Ubangiji a cikinmu idan mun dogara da bishewar Ruhunsa.


No comments:

Post a Comment