Tuesday, 7 November 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



The Introduction to the Hausa Version of my Book "Everyday With the Holy Spirit" I believe the Hausa Readers will be blessed immensely by it in Jesus Name...

BISHEWAR  RUHU  MAI TSARKI
Gabatarwa
Na dade ina tunani da ganin Kirista masu yawan gaske suna rayuwa da aikin Ubangiji ba tare bishewar Ruhu Mai Tsarki ba. Kamar yadda Manzo Bulus ya gane a cikin rayuwar wadansu a cikin Ayyukan Manzanni 19:1-6. Ya tambaye su,   “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa'ad da kuka ba da gaskiya?”  Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.” Wannan ita ce matsalar da nake gani a cikin masu bin Yesu dayawa a cikin Ikilisiyoyinmu.

Babbar  matsalar da ta jawo wannan damuwar ita  ce rashin koyaswar gaskiya. A kashin gaskiya, Ikilisiyoyi da dama ba su sami kafuwa a bisa tushen koyaswa da irin rayuwar Yesu Almasihu ba. Ina nufin koyaswa akan bangaskiya da ta bishewar Ruhun Ubangiji. A maimakon haka aka fi bada fifiko akan rukunai da ka’idodin mutane suka shishirya.  

Inda babu Ruhu Mai Tsarki kaucewa daga gaskiya a fili ta  ke. Ga misali a cikin Matiyu 24:11. Annabawan karya, ai sune wadanda suka san gaskiya amma sun ki su koyar da kuma aikatawa. A takaice, an bayyana irin wadannan halayen a cikin 2 Timotawus 3:5,7.  Ga ibada amma ana musun ikon Ruhun Ubangiji, ga koyaswar Littafi Mai Tsarki da ayyukan Ikilisiya amma babu tabbacin gaskiyar!  

Wadannan da wadansu dalilai dayawa suka sa aka wallafa wannan ‘yar takarda. Ya kamata masu bin Almasihu su sani cewar akwai ayoyin Littafi Mai tsarki dayawa da suka ambaci Ruhu Mai Tsarki da irin ayyukansa da suka wajaba Masu bin  su yi koyi da su. Wannan zai kawar da hujjar bin koyaswar mutane fiye da abin da ke a rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki.

No comments:

Post a Comment