Monday, 27 November 2017

BISHEWAR RUHU MAI TSARKI



BISHEWAR RUHU MAI TSARKI (BABI NA 4)
MAIMAITAWAR SHARI'A
 34:9  "Joshuwa ɗan Nun yana cike da Ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa." 1Kor 12:8 Ya ambaci Ruhun hikima, daya daga cikin baye-bayensa. Kamar yadda na fada  a aya ta 27:18, dibiya hannun da Musa yayi wa Joshu’a shaida ce cewar shi zabbaben Ubangiji ne  ta bishear Ruhu Mai Tsarkin.

Wannan ya zama dole sauran jama’a su yi biyyaya da shi. Ba mamaki, ana iya samun tawaye da rashin yarda da yawa inda babu shugabancin bishewar Ruhu Mai Tsarki.   

No comments:

Post a Comment